MENE NE LABARI
Labari shine duk abin da mutum zaiji ko ya gani ko ya karanta wanda zai burge ko bada mamaki ko haushi ko jimami da sauransu. A takaice dai duk wani al'amari da zai ja hankalin mutum ana iya kallonsa a matsayin labari. Kamar yadda muka fada a baya, marubuci ne ke iya zakulo labari mai ma'ana da ke iya jan hankali.
HANYOYIN SAMUN LABARI
Akwai hanyoyi da dama ake iya samun labari daga gare su. Hanyoyin kuwa sun hada da:
a. Gani da ido
b. Faruwar wani abu akan mutum
c. Jin labari a kafafen watsa labarai ko daga bakunan mutane.
d. Karatu littatafai da nazari
e. Mafarki
f. Bincike
g. Tunani da hasashe da sauransu
YADDA AKE TSARA LABARI
Ya zama wajibi ga mai rubutun film ya tsara labarinsa daki-daki tare da jera abubuwan da zasu faru tun daga farko har karshe. Abu ne mai kyau marubuci ya san farkon labarinsa, tsakiyarsa da kuma karshensa yadda zai bada maana kuma ya yi armashi.
YADDA AKE AUNA LABARIN FIM
Kowanne labarin da za a mayar da shi film sai an auna shi kan wani sikeli da masana fannin suka kira *Paradigm* wanda wajibi ne labari ya cika wadannan sikeli daidai. Ma'aunin da ake auna labarin kuwa shi ake kira *Three Act Structure* watau shika-shikai uku na ingantaccen labarin fim.
Idan na ce ingantacce ba ina nufin labari mai nuna kyawawan dabiu ba ko sharholiya ba, ina nufin labarin da zai dau hankali wanda mai kallo zai gaza tashi har sai ya ga karshe. Labarin da zai sa mai kallo ya kasa kauda kansa ya zama cike da dokin son ganin abin da zai auku nan gaba. Ba a so marubuci ya ba wa mai kallo damar cankar abin da zai faru nan gaba, an fi so kodayaushe marubuci ya ba wa mai kallo ko karatu mamaki ta hanyar nuna masa wani abu da bai yi zato ba. Wannan shi ne ingantaccen labari.
Yadda ake samar da ingantaccen labari shine matakan da ake kulla zaruruwan abubuwan da za su faru ta fuskar tambaya da amsa. Irin wannan salo ana kiransa *What happens next* watau yin tunanin abin da zai faru daga mataki zuwa mataki. A mako mai zuwa za mu yi cikakken bayani kan wannan tsari na *three act structure*
MATAKAN RUBUTA LABARI
Rubuta ingantaccen labari yana bukatar bin wadannan matakan:
*Idea* - Watau tunani kan irin labarin da za a rubuta. Na bayyana hanyoyin da ake samun idea tun dazu.
*Pitch* - Dan takaitaccen bayani gamw da labarin. Misali, ina son bayar da labari akan malamin makaranta. Pitch dina zai zama... *Wani malamin makaranta da kudin albashi bai ishe shi ba kuma ba shi da wata sana'a ga shi matarsa ta mutu yana neman aure*
*Synopsis:* Takaitaccen bayanin labarin a dunkule inda za a fara da farkon labarin, tsakiyarsa da kuma karshensa.Yawanci baya wuce shafi daya na takardar full scalp.
*Character development:* Samar da manyan taurari da irin dabiunsu da shekarunsu tare da duk wani bayani da zai sa a gane su cikin sauki. Za mu yi cikakken bayani akan wannan nan gaba.
*Block ko Treatment:* Wannan shi ne mataki na bi da bi na duk abin da zai faru cikin labarin daga farko har zuwa karshe. Anan ne ake fayyace *Three Act structure* wanda na ce zan yi bayaninsa mako mai zuwa Yawanci ana rubutun ne a wani kati da ake kira index card. To amma yanzu da cigaban kimiyya ya zo, ana rubutun ma a manhajojin rubutu kamar microsoft word da sauransu.
*Mu lura da kyau, wadannan matakan da na ambata a sama, ana so kowanne marubuci ya fahimcesu su kuma ya rika amfani da su yayin kowanne irin rubutun kirkira.*
RUBUTUN LABARI.
Abu na gaba shi ne rubuta labarin da aka bi matakan can da na ambata zuwa tsarin fim (Scriprwriting ko Screenwriting). Shi rubutun fim iri biyu ne; akwai wanda ake kira
*Generic* da kuma wanda ake kira *Spec* ko *Production script*
Generic shi ne wanda marubuci ke rubutawa kai tsaye ba tare da iyakancewa ba. Kila ma marubucin ya rubuta ne a kashin kansa saboda shaawa ba tare da wani ya sa shi ba. Don haka ba a bukatar ya fayyace wasu abubuwan da babu su, misali siffanta kamannin tauraro, yanayin gida, launin mota, tsayuwar kyamera da sauransu. Sai dai idan ababen na da alaka da tasirin labarinsa.
*Spec* ko *Production* kuwa, darakta ne ke zama ya sake rubuta labarin da marubuci ya yi zuwa gwargwadon yadda yake so ya zama a aikace. Anan zai bayyana komai da komai dalla - dalla tare da bayyana irin tauraron da yake so ya zauna a labarin da kuma tsayuwar camera da awon gani da sauransu. Sai dai ya zama tilas darakta ya yi la'akari da awon labari da irin rawar da taurari suka taka. Ba abu ne mai kyau ba, marubuci ya zabi tauraro dan shekara 25, shi kuma darakta ya musanya da wani dan shekara15 ko 50. Irin wannan shi ke bata labari.
SALON RIKE MAI KALLO
Ana kiransa da *what happens next* dabara ce ake tsarawa wajen yanyanka labari yadda kafin a gama warware matsala guda an afka wata, ana warware wannan kuma sai wata mai girma ta zo. A haka har a zo karshen labarin.
Wannan salo na sa mai kallo ya bata lokacinsa yana kallon film ba tare da ya gajiya ba. Misali, ana cikin nuna tauraron a folis an tsare shi sai a katse a nuna wani wajen kuma can ana jiransa za a daura masa aure. Ashe wasu kuma ba sa so a daura auren da shi. Ana shawarwarin fasawa sai ga shi ya zo da waliyansa. Kun ga anan an warware matsalar folis kuma za a shiga wata. Kila ta yiwu a wajen akwai wadanda ba sa son a yi auren, kuma ya sansu. Suna ganinsa sai su firgita su shiga kame - kame. Anan mai kallo zai yi fatan ya nuna su ko ya muzanta su, to amma marubucin sai ya yi wuf ya canja akalar labarin ta wata fuska da ba a yi tsammani ba.
Idan kana son tsara labarinka daki - daki, to sai ka soma da sanin farkonsa da karshensa, daga nan sai ka shiga fadada labarinka ta hanyar *what happen s next*.
Idan mun dauki misali, labari akan fataucin miyagun kwayoyi.
Za mu iya farawa da amsa tambayar, *me zai faru idan ana sha ko fataucin kwayoyi?*
Daga nan fa? *Me zai faru ga mahukunta wajen bincike?*
Daga nan fa? *Me zai faru idan an zo kame?*
Daga nan fa? Haka dai har ka je karshen labahrinka.
Wannan salon ma yana da amfani har ga masu rubuta novel.
Nagode
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
DABARUN RUBUTUN FILM
MENE NE LABARI Labari shine duk abin da mutum zaiji ko ya gani ko ya karanta wanda zai burge ko bada mamaki ko haushi ko jimami da sauransu...
-
MENE NE LABARI Labari shine duk abin da mutum zaiji ko ya gani ko ya karanta wanda zai burge ko bada mamaki ko haushi ko jimami da sauransu...
-
KANNYWOOD PARTNERS Working as a team is very important in film industry. My partners are: -iStudios Multimedia Ltd -Al`umma Motion Pictu...
-
KNOW WRITER FIRST A screenplay writer or screenwriter is a writer who practices the craft of screenwriting, writing screenplays on mass med...
gaskiya naji dadin wannan rubutu naka, Allah ya kara basira.
ReplyDeletekuma na amfani haka sosai
Allah saka da Alheri
ReplyDeleteMungode Allah kara fasaha.
ReplyDelete